in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin: Fannin makamashi za'a fi baiwa fifiko a hadin gwiwar Sin da Habasha
2018-05-18 10:34:31 cri
Jakadan kasar Sin a Habasha Tan Jian ya bayyana a lokacin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanakin baya cewa, kasar Sin tana ganin batun makamashi ne ya fi zama fanni mafi muhimmanci da za'a baiwa fifiko karkashin cikakkiyar hadin gwiwar Sin da Habasha.

Tan ya ce, ana bukatar makamashi wajen yaki da talauci da bunkasa tattalin arzikin kasa, a daidai lokacin da kasar Habasha ke kokarin samar da babban rukunin masana'antu tare da tallafin kasar Sin.

Ya ce kasar Sin tana kokarin karfafawa kamfanoninta gwiwa da su zuba jari a fannin makamashi a kasar Habasha, musamman a hanyoyin samar da lantarki ta hanyar iska da kuma ta ruwa don kyautata fannin lantarkin kasar ta Habasha.

Kamfanonin kasar Sin suna sahun gaba wajen gudanar da ayyukan samar da makamashi a kasar Habasha, wadanda suka hada da aikin samar da lantarki mai karfin megawatts 6,450 ta hanyar amfani da ruwa wanda a halin yanzu ake gudanar da aikin ta tekun Blue Nile, da aikin samar da megawats 51 ta Adama I da megawats 153 ta Adama II ta hanyar amfani da iska, da kuma aikin samar da lantarki mai karfin megawats 300 na Tekeze ta hanyar amfani da ruwa.

A halin yanzu ana gudanar da ayyuka masu yawa na samar da lantarki a kasar Habasha, inda ake fatar bunkasa lantarkin kasar daga karfin megawats 4,300 da ake dashi a halin yanzu zuwa karfin megawatts 17,300 nan da shekarar 2020.

A yayin da taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato (FOCAC) ke karatowa wanda za'a gudanar a watan Satumba a birnin Beijing, Tan ya bayyana cewa, batun zurfafa hadin gwiwar Sin da Habasha a fannin makamashi shine zai mamaye ajandar tattaunawa tsakanin kasashen biyu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China