Wannan kara dai ta sha banbam da saura, saboda tana neman kasar Italiya ta biya diyya kan matakan da kasar Libya ta dauka, dangane da zargin da ake mata na keta 'yancin bil-Adama.
Su dai 'yan Najeriyar sun tsira ne a kokarin da suke na tsallakawa kasar Italiya a shekarar da ta gabata, tafiyar da suka ce na cike da hadari sakamakon tsauraran manufofin Libya masu cike da hadari da kasar ta dauka na kokarin tilastawa 'yan gudun hijira da jiragen ruwan dake dauke da bakin haure komawa yankin ruwan Afirka
Wannan manufa dai wani bangare ne na kokarin da mahukuntan kasar Italiya ke yi na hana bakin haure daga kasashe matalauta da wadanda ke fama da yake-yake a Afirka da yankin gabas ta tsakiya shiga kasar.(Ibrahim)