Stephane Dujarric, kakakin sakatare janar na MDD ya ce, mista Guterres ya nuna gamsuwa da salon shugabancin shugaban kasar Jose Mario Vaz, da kuma yadda manyan jam'iyyun siyasar kasar ke tafiyar da harkokinsu.
Sanarwar ta ce, babban jami'in MDDr ya bukaci dukkan bangarorin kasar da su hada kai wajen kaiwa muhimmin mataki na gaba, da suka hada da kafa gwamnatin hadin kan kasa, da sake bude majalisar dokokin kasar, da kuma aiwatar da ragowar yarjejeniyar da aka cimma ta Conakry.
Guterres ya ce, MDD za ta ci gaba da yin aiki tare da kungiyoyin shiyya wajen tallafawa sake gina zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma mara baya ga dukkan kokarin ci gaban kasar ta Guinea-Bissau. (Ahmad Fagam)