in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Reshen jiragen sama masu saukar unkulu na kiyaye zaman lafiya na kasar Sin ya gama aikin jigilar sojojin tawagar UNAMID
2018-03-25 13:38:57 cri
A jiya Asabar 24 ga wata, reshen jiragen sama masu saukar unkulu na shirin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin ya gama aikinsa na jigilar sojojin a sansanin Ruwanda na tawagar MDD da kungiyar AU dake yankin Darfur wato UNAMID cikin nasara.

Bisa bayanin da wannan reshen na sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin ya yi, tun daga watan Febrairu na bana, tawagar UNAMID ta fara hada yankunan aikinsu da kyautata ayyukansu, da fara canja aikin sojojin kiyaye zaman lafiya dake yankunan da dai sauransu bisa kudurin kwamitin sulhun MDD da abin ya shafa. Saboda haka, reshen jiragen sama masu saukar unkulu na kiyaye zaman lafiya na kasar Sin ya fuskanci matsin lamba mafi girma tun bayan da aka kafa shi.

Don kammala aikin jigilar sojojin sansanin Ruwanda, reshen jiragen sama masu saukar unkulu na kiyaye zaman lafiya na kasar Sin ya yi bincike kan shirin tafiya, da yadda ake raba ma'aikatan jiragen saman, da aikin bada jagoranci da sa ido, da yadda ake tafiya bisa yanayin yankunan da za a gudanar da aikin, da tabbatar da tsaro da magance duk wani hadari. A cikin kwanaki 11 da tafiyarsu, yawan awoyin da jiragen saman suka shafe suna tafiya ya kai kimanin 50, wadanda suka yi jigilar mutane kimanin 400 tare da kayayyakin da nauyinsu ya kai ton 18. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China