in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an tsaro sun shiga farautar 'yan bindiga da suka hallaka mutane a birnin Gwari
2018-05-07 20:42:05 cri

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce jami'an ta, sun dukufa wajen ganin sun cafke 'yan bindigar da suka hallaka mutane a kalla 45, a kauyen birnin Gwari dake jihar Kaduna a arewacin kasar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kaduna Mukhtar Aliyu, ya shaidawa manema labarai a Litinin din nan cewa, an kara bataliyar 'yan sandan kwantar da tarzoma 3 a yankin da wannan lamari ya auku, domin tabbatar da an damke wadanda suka aikata wannan ta'asa. Ko da yake a cewar sa ba a kai ga kama kowa ba, amma rundunar na da imanin cewa za ta bankado asirin masu laifin.

An dai hallaka mutanen 45 mafiya yawansu kananan yara, lokacin da maharan da ake zaton daga jihar Zamfara suka fito, suka yiwa garin kawanya, suka kuma cinna masa wuta, kana suka bude wuta da bindiga kan al'ummar sa kimanin su 3,000.

Da yake karin haske kan aukuwar harin, kwamishinan 'yan sandan jihar Austin Iwar, ya ce a ranar Lahadi, an binne gawawwakin mutane 45, yayin da aka tura 'yan sanda 200 yankin domin tabbatar da tsaro.

A nata bangaren, gwamnatin jihar Kaduna ta fidda wata sanarwa, tana mai cewa za a girke bataliyar sojoji musamman a yankin, domin kawo karshen yawan kashe kashe dake aukuwa.

Kaza lika mahukuntan jihar sun umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, da ta gaggauta samar da taimakon jin kai ga al'ummar da wannan hari ya shafa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China