Sanarwar da kakakinsa Stephane Dujjaric ya fitar, ta ce Joyce Msuya, za ta maye gurbin Ibrahim Thiaw na Mauritania, wanda Sakatare Janar din ya yabawa salon shugabancinsa da sadaukarwar da ya yi, yayin wa'adin aikinsa.
Har ila yau, Sakatare Janar din ya nada Joyce Msuya a matsayin mai taimaka masa.
Bisa tarihin rayuwarta da MDD ta fitar, Joyce Msuya ta taba zama mai bada shawara ga mataimakin shugaban Bankin Duniya na yankunan gabashin Asia da Pasifik. (Fa'iza Msutapha)