in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira ga dukkan bangarori a Sudan ta Kudu su saki yara sojoji
2018-05-20 13:04:54 cri
MDD ta yi kira ga bangarori masu rikici da juna a Sudan ta kudu, su saki dukkan yara sojoji tare da yin aiki tare da majalisar domin kaucewa sake amfani da kuma horar da yara a matsayin sojoji.

Wakiliyar musammam ta shirin yara a yankunan rikici na MDD, Virginia Gamba, ta ce ta samu kwarin gwiwa daga sakin yara 210 ciki har da 'yan mata 3, da 'yan tawayen bangarori masu rikici da juna suka yi a ranar Juma'ar da ta gabata.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya, Virginia Gamba, ta alakanta sakamakon da aka samu da dorewar kiraye-kirayen MDD da al'ummomin kasashen waje.

Ta ce sakin yaran 210 da aka yi a ranar Juma'a, ya kawo adadin yara da aka saki tun farkon wannan shekara zuwa 800.

An saki yaran ne daga kungiyar adawa ta SPLM-IO da kuma ta NSF, a ranar Juma'ar da gabata a yankin Pibor dake gabashin Sudan ta kudu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China