in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na inganta amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta hanyar da ta dace
2018-05-18 10:52:50 cri
Yayin bikin ranar kafofin sadarwa da bayanai ta duniya, MDD ta yi kira da a mai da hankali kan damarmakin da kwaikwayon tunanin dan Adam ta na'ura, zai yi wajen gaggauta cimma muradun ci gaba masu dorewa na majalisar.

Yayin da aka gudanar da bikin na bana a wajen taro na 2, amfani da kwaikwayon tunanin dan Adam ta na'ura, bisa hanyar da ta dace, wanda ya gudana a Geneva, hukumar kula da batutuwan da suka shafi bayanai da fasahohin sadarwa ta MDD (ITU) ta samo wani take da zai bada damar amfani da tunanin dan Adam ta hanyar da ta dace ga kowa.

A cewar Sakatare Janar na hukumar ITU, Houlin Zhao, taron farko, ya tattauna kan kyakkyawan tasirin damarmakin amfani da naurar kwaikwayon tunanin dan Adam, inda na bana zai yi amfani da yunkurin da aka yi a bara, wajen samo hanyoyin aiwatar da fasahar domin bunkasa inganci da dorewar rayuwa a duniya.

A nasa sakon, sakatare Janar na MDD Antonio Gutteress, ya yabawa ITU bisa rawar da ta taka, na rage gibin dake akwai tsakanin masu amafani da fasahohin zamani da wadanda ba sa amfani da shi, da kuma hada mutane a duk inda suke. Ya ce yayin da ake sa ran samun karin abubuwan zamani a nan gaba, ya na maraba da yadda aka bada muhimmanci ga batun lalubo hanyoyin amfani da kwaikwayon tunanin dan Adam wajen gaggauta cimma nasarar muradun ci gaba masu dorewa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China