in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya tsawaita wa'adin shirinsa na wanzar da zaman lafiya a yankin yammacin Sahara
2018-04-28 15:50:30 cri
Kwamitin tsaro na MDD ya amince da kudurin tsawaita aikin shirinsa na wanzar da zaman lafiya a yankin yammacin Sahara da watanni 6, har zuwa ranar 31 ga watan Octoban 2018.

Kudurin mai lamba 2414 ya samu amincewar 12 daga cikin mambobin kwamitin 15, inda kasashen Sin da Habasha da Rasha suka kauracewa kada kuri'ar.

Kudurin ya jadadda muhimmancin da ke akwai wajen sabunta kudurin bangarorin dake kokarin shawo kan matsalar yankin, wajen shiryawa sabon zagayen tattaunawa.

Ya kuma jadadda bukatar samuna nasara game da samar da dawwamammiyar mafita mai ma'ana da amfani, ga batun cimma yarjejeniya a yankin yammacin Sahara.

Kudurin ya bayyana damuwa game da kasancewar kungiyar Polisario wadda ke rikici da Morocco domin samun yancin yankin yammacin sahara a zirin Guerguerat dake kudu masu yammancin yakin da ake rikici a kai, inda ya yi kira da ta janye nan take.

Bayan amincewa da kudurin, Jakadan Morocco a MDD Omar Hilale ya ce babu babu wani tsarin warware rikici da za a cimma ba tare da janyewar Polisario Front daga Guerguerat ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China