Nickolay Mladenov, ya shaidawa kwamitin sulhu na MDD a jiya cewa, tabarbarewar tsaro, da na ayyukan ci gaba, da na agajin jin kai, da kuma takaddamar siyasa na iya mayar da Gaza wani wuri mai hadari. Yana mai cewa, duk da wannan yanayi, dole ne a yi dukkan mai yuwa wajen kare barkewar wani yaki a Gaza.
Cikin makonni 4 da suka wuce, dubban dubbatar Falasdinawa ne suka hadu a yankin iyakarsu da Isra'ila, karkashin zanga-zangar da suka yi wa lakabi da Great March of Return, wanda ke neman Falasdinawa dake gudun hijira su koma kauyuka da yankunansu da yanzu ke Isra'ila.
Ana sa ran za a ci gaba da zanga-zangar da za ta kai har ranar bikin 'yancin kan Isra'ila wato 14 ga watan Mayu, kuma za ta iya fadada zuwa yammacin kogin Jordan, har ma da yankunan dake gaba da shi. (Fa'iza Mustapha)