Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a hada hannu ga yunkurin taimakawa gwamnatocin kasashen duniya da al'ummominsu wajen samawa da tabbatar da dorewar zaman lafiya.
Da yake jawabi ga taron majalisar kan samar da zaman lafiya da tabbatar da dorewarsa, Antonio Guterres ya ce mataki da yanayin kalubalen da ake fuskanta, na bukatar kyakkyawan hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki, bisa la'akari da muhimman batutuwa da manufofin da kasa ke ba fifiko.
A cewarsa, wadanan masu ruwa da tsaki sun hada da gwamnatoci da MDD da sauran hukumomin kasa da kasa da kungiyoyin yankuna da cibiyoyin harkokin kudi na kasa da kasa da kungiyoyin al'umma da na mata da matasa da kuma bangarori masu zaman kansu. (Fa'iza Mustapha)