Ofishin WHO mai kula da shiyar Afirka ne ya shirya taron na kwanaki biyu, bisa taken, "ba da muhimmanci ga jama'a: Taswirar inganta harkokin kiwon lafiya a nahiyar Afirka".
Bugu da kari, ana fatan taron zai bullo da sabbin matakan hadin gwiwa kan yadda za a samar da kiwon lafiya ga jama'a, da yadda jama'a za su samu kulawar lafiya cikin rahusa.
A jawabinta na bude taron Darektan ofishin WHO mai kula da shiyyar Afirka Matshidiso Moeti ta ce taron wani muhimman mataki ne na ci gaban da ake samu a fannin hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, da nufin ciyar da ajendar kiwo lafiyar nahiyar gaba.
Ana saran gudanar da jerin shirye-shirye da suka shafi daukar nauyin harkokin kiwon lafiya, tsaron kiwon lafiyar kasa da kasa, bincike da yayata batutuwan da suka shafi kiwon lafiya da sauransu.(Ibrahim)