Michel Sidibe, mataimakin magatakardan MDD kuma daraktan hukumar tsara shirin yaki da cutar sida ta MDD ya bayyana a kwanan nan, cewar MDD za ta koyi fasahohin kasar Sin wajen horar da unguzomomi miliyan biyu a kasashen Afirka nan da shekarar 2020. Domin cimma wannan buri, MDD ta tsara shirye-shirye goma, tare da fatan kasar Sin za ta taimaka da fasahar da ta samu a fannin ma'aikata masu aikin jiyya a matakin farko wajen taimaka wa kasashe masu karami da matsakaicin karfi wajen aiwatar da shirin.(Kande Gao)