in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu bakin fada a ji a fannin kimiyya da fasahar kere-kere a shekarar 2017
2018-01-29 10:00:56 cri

Shugaban kungiyar kimiyya da fasahar kere-kere ta kasar Sin (CAST) Wan Gang ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance a sahun gaba a fagen kimiyya da fahasar kere-kere a duniya a shekarar 2017 da ta gabata.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron da kungiyar ta shirya a Jumma'ar da ta gabata, inda ya tabo kadan daga cikin masanan kasar Sin da suka samu manyan matsayi a kungiyoyi na kasa da kasa a shekarar da ta gabata.

Jami'in yaba da misali da Gong Ke, shugaban jami'ar Nankai kana kwararre a fannin injiniyan latoroni wanda aka zaba a matsayin shugaban kungiyar injiniyoyi na duniya mai hedkwata a birnin Paris, inda ya zama masanin kasar Sin na farko da ya taba shugabantar kungiyar.

Bugu da kari, a shekarar 2017, CAST ta gudanar da aikin gina cibiyoyin hadin gwiwa na kasa da kasa tsakanin kungiyoyin kimiyya na kasashen da ke cikin shawarar ziri daya da hanya daya, dandalin da ya samar da cibiyoyin bincike da samun horo 10 wanda ya shafi kasashe 63 dake cikin wannan shawara.

A cewar Wan, kudaden da kasar Sin ta ware a fannin bincike a shekarar 2017 da ta gabata, shi ne na biyu a duniya, kana abubuwan da aka kirkiro sun kasance a kan gaba sau bakwai a jere.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China