Cibiyar kera linzamai ta Sin ta ce kamfanin dake karkashinta na China Rocket, na shirye-shiryen aiwatar da shirin.
Wata sanarwa da cibiyar ta CALT ta fitar na cewa, za a kera kananan linzaman ne ta yadda za su kasance masu karfi da tabbacin aiki da kuma arha, sannan ba za su bukaci dogon lokacin kaddamarwa ba.
A cewar cibiyar, linzami na iya daukar nauyin kilogram 100 zuwa 500, kuma yana da saukin sarrafawa.
Tun bayan kaddamar da ita a shekarar 1957, CALT ta kasance cibiya mafi girma dake samar da linzamin roka. Ita ce kuma ta kera roka Long March da ya samu karbuwa a duniya.
A cewar cibiyar, bukatar harba tauroron dan Adam a duniya domin kasuwanci za ta zarce 10,000, yayin da bukatar a cikin gida za ta kai 1,000. Su ma manyan kamfanonin fasaha na kasar na shirin harba tauraron dan Adam. (Fa'iza Mustapha)