in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana kimiyya na kasar sin sun gano wani yanki mai arzikin sinadaran REE a tekun Fasifik
2018-04-02 10:51:37 cri

Wani ayarin masana kimiyya na kasar Sin, sun gano wani babban yanki mai arzikin sinadaran karkashin kasa da ake kira da Rare Earth Elements wato REE a takaice, a yankin kudu maso gabashin tekun Fasifik.

A wata kwarya-kwaryar mataki, masana kimiyyar sun shata wani yankin dake da arzikin sinadaran, mai fadin murabba'in kilomita miliyan 1.5 a can kasan kudu maso gabashin tekun Fasifik.

Gano yankin zai taimaka wajen nazarin sinadaran na REE da kuma binciken muhallin karkashin teku.

Ayarin masanan ya kammala bincikensa na farko cikin ruwa a kudu maso gabashin tekun Fasifik, inda suka kuma tattaro samfurin albarkatun karkashin teku da ma ruwan tekun da bayanan da suka hada da yanayin saman teku da sinadaran ban kasa da na ruwa da bayanan yanayin sararin samaniya da kuma dangantakar sinadarai da halittu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China