in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta haramta hadawa da shigar da Kodin a cikin kasar
2018-05-02 09:50:27 cri
Gwamnatin Najeriya ta ce ta haramta hadawa da shigar da magungunan tari masu kunshe da Kodin a cikin kasar, a wani mataki na kawo karshe yadda ake amfani da maganin ba bisa ka'ida ba, musamman tsakanin matasa.

Ministan lafiya na tarayyar Najeriya Isaac Adewole ya ce, gwamnati ta umarci hukumomin da abin ya shafa, da su aiwatar da wannan haramci, wanda ya hada da dakatar da ba da iznin shigo da sinadarin na Kodin da ake amfani da shi wajen hada maganin tari.

Bugu da kari, ministan ya ce gwamnati ta haramta sayar da duk wani maganin tari mai kunshe da Kodin ba tare da izinin likita ba.

A cewarsa, an kuma umarci hukumomin gwamnati da su sanya ido kan yadda za a rika sanya alama a jikin maganin da yadda ake sayar da maganin tari mai kunshe da Kodin a dukkan fadin kasar.

Gwamnati dai ta dauki wannan mataki ne, biyo bayan wasu rahotanni game da yadda ake samun karuwar ta'ammali da wadannan magungunan a Najeriya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China