in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu ta ce nada sabon jakadan Amurka a kasarta zai kyautata mu'amalar kasashen biyu
2018-04-13 11:04:44 cri

Gwamnatin Sudan ta kudu ta sanar da cewa matakin da Amurka ta dauka na nada sabon jakadanta a Sudan ta kudu zai taimaka wajen kyautata mu'amala tsakanin kasashen biyu.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Mawien Makol, ya ce wannan mataki da Amurka ta cimma na nada Thomas Hushek domin ya zama jakadan Amurkar a Juba zai kyautata dangantaka a tsakanin kasashen biyu wanda a 'yan kwanakin nan ta yi tsami, tun bayan da Amurkar ta kakabawa kasar takunkumi kan wasu manyan jami'an gwamnati da wasu kamfanonin kasar.

Makon ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Juba cewa, da ma dai akwai huldar diplomasiyya tsakanin Sudan ta kudu da Amurka. Don haka suna matukar farin ciki da Amurkar ta tura wani jami'in wanda zai jagoranci ofishin jakadancinta a kasar. Ya ce ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta kudun tana maraba da shi, kuma za ta yi aiki tare da shi.

Wannan mataki dai ya zo ne bayan da kwamitin hulda da kasashen waje na majalisar dattijan Amurkar a zamansa na ranar Laraba ya amince da nada Hushek wanda shugaban Amurka Donald Trump ya gabatawa majalisar a matsayin mutumin da yake son nadawa jakadan Amurka a Sudan ta kudu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China