in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta ce komawar 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu gidajensu na da matukar hadari
2018-03-21 10:59:48 cri
Wata babbar jami'ar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta ce halin da ake ciki a yanzu a Sudan ta kudu abu ne mai matukar hadari ga miliyoyin 'yan gudun hijirar da yakin basasar kasar ya raba su da matsugunansu su fara komawa gidanajensu a halin yanzu.

Maria Corinna Miguel Quicho, mataimakiyar jami'in bada kariya na hukumar ta UNHCR a Sudan ta kudu ta ce, ko da yake, da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar na Sudan ta kudu suna dokin sake komawa gidajensu, amma halin da ake ciki a kasar a yanzu yana da matukar hadari a mayar da mutanen zuwa gidajensu sakamakon yawaitar tashe tashen hankula da ake cigaba da samu a kasar da kuma rashin kayayyakin amfani da ake bukata na yau da kullum.

Ta ce a halin yanzu ba za'a fara sake tsugunar da mutanen da rikicin ya daidaita ba, kasancewar har yanzu ana ci gaba da jin karar harbe-harben bindigogi, zaman lafiya shi ne abu mafi muhimmanci, kuma za'a iya sake mayar da mutanen ne bisa sharadin samun kyautatuwar yanayin tsaro da kwanciyar hankali, Quicho ta fadawa 'yan jaridu a lokacin taron karawa juna sani na wuni biyu wanda MDD ta dauki nauyinsa, wanda ya mayar da hankali game da shawo kan matsalolin da suka shafi mutanen da rikicin Sudan ta kudu ya raba da matsugunansu.

Ta kara da cewa, tana fatan duk wanda yake son komawa gida ya sake tunani. Ta ce zai fi kyautuwa su zauna a sansanin 'yan gudun hijirar maimakon komawa gidajensu a yanzu.

Sudan ta kudu ta fada cikin tashin hankali ne sama da shekaru 4 da suka gabata, lamarin da ya wargaza yanayin zaman lafiyar jama'ar kasar.

MDD ta yi kiyasin sama da mutanen kasar miliyan 2 ne rikicin ya tilastawa yin hijira zuwa makwabtan kasashe, kana wasu mutane kimanin miliyan 1.9 ke neman mafaka a yankunan kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China