in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci sassan dake fada da juna a Sudan ta kudu da su martaba yarjejeniyar da suka cimma
2018-05-04 09:41:41 cri
Tawagar dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu ko UNMISS a takaice, ta yi kira ga bangarorin dake fada da juna a kasar, da su mutunta yarjejeniyar da suka sanyawa hannu a shekarar da ta gabata.

Wakilin musamman na babban sakataren MDD kana shugaban tawagar ta UNMISS David Shearer shi ne ya yi wannan kiran, inda ya yi gargadin cewa, akwai fargabar ci gaba da tashin tankali a jihar Unity duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma.

Da yake karin haske cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a daren Laraba bayan wata ziyarar da ya kai kasar, jami'in da wata tawaga daga UNMISS sun gana da shugabannin gwamnati da na bangaren 'yan adawa dake yankin, inda ya bukace su da su ajiye makamansu su kuma sasanta, kana su yi aiki tare don ganin sun samar da dauwamammen zaman lafiya.

Ya ce, yarjejeniyar da suka sanyawa hannu a shekarar da ta gabata ta karfafa shirin samar da zaman lafiya, amma kuma muddin babu niyyar aiwatar da ita, to ba za ta je ko'ina ba. Ya ce tawagar UNMISS za ta ci gaba da sauke nauyin dake wuyanta na ci gaba da kare rayukan fararen hula, da ma ganin shirin samar da zaman lafiyar da aka cimma ya fara aiki. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China