in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu ta nemi MDD ta ayyana sunayen manyan jami'an da ake zargi da cin zarafin fararen hula
2018-03-01 10:08:24 cri
Wani kusa a gwamnatin Sudan ta kudu ya bukaci MDD ta sanarwa jama'a sunayen manyan jami'an sojoji sama da 40 da ake tuhuma da laifin cin zarafin al'umma a tsawon shekaru sama da 4 tun bayan da kasar ta afka cikin yakin basasa, kamar yadda rahoton kwamitin kare hakkin dan adam na MDDr ya ambata.

Mai magana da yawun shugaba Salva Kiir, na kasar Sudan ta kudun Ateny Wek Ateny, ya ce basu da masaniya game da sunayen dakarun rundunar sojin (SPLA) na Sudan ta kudun wadanda suka hada da manyan janar janar din soji 17, da Birgediya janar 8, da kanal din soji 8, da kuma gwamnonin jahohi 3, wadanda hukumar kare hakkin dan adam ta MDDr ke gudanar da bincike kansu a Sudan ta kudun.

Ateny ya fada a Juba cewa, an sanar da su cewar ana tuhumar jami'an sojoji sama da 40 da laifukan cin zarafin, amma ba'a sanar da su sunayen jami'an ba. Don haka suke bukatar MDDr data ayyana sunayen jami'an tare da kwararan hujjoji, ya kara da cewa, suna dakon ganin an mika musu sunayen jami'an domin tabbatar da cewa ko akwai cin karo da juna game da rahoton da aka fitar a lokutan baya.

A ranar 23 ga watan Fabrairu ne kwamitin binciken take hakkin bil adama na MDD ya fitar da rahotonsa, inda ya nuna cewa an samu manyan jami'an sojojin da laifin cin zarafi da keta haddin fararen hula a lokacin tashin hankalin kasar tsakanin shekarar 2016 da 2017.

An riga an mika sunayen mutanen 41 da ake zargi ga ofishin babban jami'in hukumar kare hakkin dan adam ta MDDr, Zeid Ra'ad Al Hussein.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China