Kakakin Shugaban kasar Femi Adeshina ne ya bayyana haka a jiya Juma'a, inda ya ce shugabannin biyu za su gana game da hanyoyin inganta dangantaka a tsakanin kasashensu da kuma batutuwan da suke mayar da hankali kai da suka hada da habaka tattakin arziki da yaki da ta'addanci da sauran barazanar tsaro.
Femi Adeshina, ya ce Shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki ne bisa gayyatar da Shugaba Trump ya yi masa.
Muhammadu Buhari zai bar Abuja babban birnin kasar ne a yau Asabar, inda kuma zai gana da Shugaba Trump a yau din.
Kakakin Shugaban ya ce, an kuma shirya wasu taruka tsakanin manyan jami'an gwamnatin Nijeriya da shugabannin manyan kamfanonin Amurka a bangarorin aikin gona da sufurin jiragen sama da kuma sufuri baki daya.
Ya ce an shirya ganawa tsakanin jami'an Nijerya da na Boeing, Kamfanin kera jirgin sama mafi girma a duniya, game da aikin kera jirgin sama mallakar Nijeriya. (Fa'iza Mustapha)