in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 27 sun mutu sanadiyyar wasu tagwayen hare-hare a Nijeriya
2018-05-02 09:47:55 cri
Gwamnatin jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Nijeriya, ta tabbatar da cewa, wasu tagwayen hare-hare sun yi sanadin mutuwar mutane 27 tare da jikkatar wasu 56, a garin Mubi na jihar.

Wata sanarwa da Kwamishinan yada labaran jihar, Ahmad Sajoh ya fitar, ta ce an kwantar da mutanen 56 da suka jikkata a asibiti, yana mai cewa 'yan kunar bakin wake biyu ne suka kai hare-haren.

A cewarsa, bam na farko ya tashi ne a wani masallaci, yayin da maharin na biyu, ya ta da nashi a wata kasuwar gwanjo dake kusa da masallacin da aka kai wa hari na farko.

Ko cikin watan Nuwamban bara, a kalla mutane 50 sun mutu sanadiyyar wani harin da aka kai wani masallaci a garin na Mubi.

MDD ta ruwaito cewa, tun daga shekarar 2009, kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram, ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 20,000. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China