in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya
2018-04-27 17:27:45 cri

A yau Juma'a da yamma ne a birnin Wuhan, hedkwatar lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya Narendra Modi wanda ke ziyara da kashin kai a kasar Sin.

Shugabannin kasashen biyu sun fara ganawa ne a dakin adana kayayyakin tarihi na lardin Hubei. A yayin da shugabannin biyu suka kalli al'adun mai dadadden tarihi na kasar Sin, musamman al'adun yankin Jin da Chu, sun kuma yi musayar ra'ayoyi kan yadda kasashen Sin da Indiya, wato tsoffin kasashe masu dadadden tarihin wayin kai za su kara yin ma'amalar al'adu ta yadda za a tabbatar da ganin al'adu daban daban za su iya zaman tare cikin lumana. Shugabannin biyu sun ci gaba da yin shawarwari a otel din tafkin Donghu.

Kamar yadda gwamnatocin kasashen Sin da Indiya suka tsaida, shugaba Xi Jinping da firaminista Modi za su yi shawarwari na kashin kai a birnin Wuhan daga yau Jumma' zuwa gobe Asabar 28 ga wata, inda za su yi musayar ra'ayoyi kan babban sauyin da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 100 da suka gabata a fadin duniya, har ma da batun yadda za a bunkasa dangantaka daga dukkan fannoni a nan gaba tsakanin kasashen biyu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China