A lokacin ziyarar aiki da ya kai Habasha, mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao, ya ce Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin wato CPC, da jam'iyyar Ethiopian People's Revolutionary Democratic Front (EPRDF), sun gudanar da musayar dabaru na hadin gwiwa da kuma karawa juna sani
Da yake zantawa da mataimakin Firaiministan kasar Habasha Demeke Mekonnen, wanda kuma shine mataimakin shugaban jam'iyyar ta EPRDF, Li, ya bukaci a kara zurfafa dangantaka da musayar kwarewa a tsakanin bangarorin biyu, domin samun gagarumin cigaba ta fuskar kyakkywar mu'amala dake tsakanin kasashen biyu.
Ya kara da cewa, jam'iyyar CPC ta kasar Sin da gwamnatin Sin, za su aiwatar da sakamakon da aka cimma a lokacin taron dandalin hadin kan Sin da Afrika wato (FOCAC), wanda ya gudana a watan Dismabar bara a birnin Johannesburg, wanda hakan zai taimaka wajen cigaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Habasha.(Ahmad)