Da yake jawabi yayin da Mr. Li Yuanchao ke ziyarar aiki a kasar ta Habasha, Hailemariam ya ce irin dogon lokaci da kasar Sin ta shafe tana tallafawa Habasha ta hanyoyi daban daban na inganta ci gaba, ya shaida irin nasarar da kasashen suka cimma wajen tabbatar da cin moriyar juna.
Kaza lika Hailemariam, wanda kuma shi ne shugaban jam'iyyar EPRDF mai mulkin kasar, ya ce jam'iyyar sa na fatan koyi daga dimbin nasarori, da kwarewar da JKS ta nuna, wajen gudanar da managarcin salon mulki a kasar Sin.
Shi kuwa a nasa bangare, mataimakin shugaban kasar Sin jinjinawa mahukuntan kasar ta Habasha ya yi, bisa abun da ya kira babban ci gaba da suka samar ga kasar karkashin jam'iyyar EPRDF mai mulki, cikin shekaru sama da 25 da suka gabata.
Mr. Li Yuanchao ya ce Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa tare da Habasha wajen aiwatar da yarjeniyoyin da shugabannin sassan biyu suka cimma, da ma kudurorin da aka amince da su, yayin taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC wanda ya gabata a watan Disambar bara a Afirka ta Kudu.
Li ya kara da cewa, JKS na fatan zurfafa alaka tsakanin jam'iyyun kasashen biyu, ta yadda za su ci gajiyar kwarewar su a fannin jagoranci, da ma sauran muhimman dabaru na wanzar da ci gaba.(Saminu Alhassan)