A wajen taron manema labaru da ya gudana a jiyan, mista Kalenga ya ce, cikin kwanaki 42 da suka wuce, ba a gano karin mutum ko daya da ya kamu da cutar Ebola a kasar ba. Da ma hukumar lafiya ta duniya ta kayyade cewa, idan ba a samu karin wasu mutanen da suka kamu da cutar cikin kwanaki 42 a jere ba, to, za a iya sanar da kawo karshen annobar.
A cewar jami'in, annobar Ebola da ta barke a Congo Kinshasa a wannan karo, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 4. A madadin kasarsa, jami'in ya nuna godiya ga kungiyoyin kasa da kasa, gami da gwamnatin kasar Sin, wadanda suka kai dauki ga jama'ar kasarsa.
An fara gano barkewar annobar Ebola a kasar Congo Kinshasa a ranar 12 ga watan Mayun bana, wanda ya kasance karo na 8 da kasar ta sha fama da cutar Ebola tun daga shekarar 1976. Bayan da aka sanar da barkewar cutar Ebola a kasar a wannan karo, gwamnatin kasar Sin ta baiwa Congo Kinshasa taimakon dalar Amurka dubu 200, da kuma sauran wasu kayayyakin da za a iya amfani da su wajen baiwa mutane kariya daga kamuwa da kwayoyin cutar Ebola.(Bello Wang)