in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Saliyo ya sha alwashin gudanar da gwamnati wadda za ta yi yaki da rashin da'a
2018-05-13 15:33:23 cri
Sabon shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio, ya yi alkawarin gudanar da gwamnati, wadda za ta maida hankali matuka ga yaki da rashin da'a, tare da baiwa kowa damar ba da gudummawa yadda ya kamata.

Shugaba Maada Bio ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, cikin jawabin da ya gabatar na bikin kama aiki da ya gudana a filin wasa na Siaka Steven dake birnin Freetown. An dai zabi shugaba Bio ne a babban zaben kasar na ranar 31 ga watan Maris.

Da yake bayyana kudurorin gwamnatinsa, shugaba Bio ya jaddada aniyarsa, ta rungumar daukacin 'yan kasar ba tare da nuna wani banbanci na siyasa ko bangaranci ba.

Daga nan sai ya jaddada manufar sa, ta baiwa 'yan kasar damar samun ilimi mai inganci kyauta, manufar da a cewarsa, ke kan gaba a jerin manyan kudurori da gwamnatinsa ke fatan samun nasarar su.

Shugaba Bio ya ce duk da irin matsanancin halin tattalin arziki da ya tarar da Saliyo a halin yanzu, yana da kyakkyawan fatan cewa, zai cimma nasarar dora kasar a kan turba ta gari.

Ya kuma ce gwamnatinsa za ta yi amfani da wasu hanyoyi 3 wajen yakar rashin da'a, da cin hanci da rashawa, da kuma fatara.

Shugaban na Saliyo ya ce, samarwa matasa ayyukan yi, zai zamo kan gaba a manyan manufofin sabuwar gwamnatin. Kana ya alkawarta kyautata alakar dake tsakanin kasar tasa da sauran kasashen duniya. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China