in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika sun dauki matakai na ko-ta-kwana bayan rahoton bullar cutar Ebola a DRC
2017-05-21 13:25:38 cri

Kasashen Afrika da suka hada da Rwanda, Uganda, Ghana, Kenya da Nigeria, suna daukar tsauraran matakai a kan iyakokinsu tun bayan samun rahoton bullar annobar cutar Ebola mai saurin kisa a Jamhuriyar demokuradiyyar Congo.

A kasar Ghana, hukumar kiwon lafiya ta bada sanarwa a Juma'ar data gabata inda tayi gargadi game da barkewar cutar ta Ebola, kana ta bukaci daraktocin shiyya dasu zauna cikin shirin ko-ta-kwana.

Sanarwar wanda Dr. Anthony Nsiah-Asare, babban daraktan kula da lafiya na kasar ya fitar, ya umarci daraktocin lafiya na kasar da su tsaurara bincike kuma da zarar sun ga wata alama ta cutar su hanzarta daukar matakan da suka dace ba tare da bata lokaci ba da nufin dakile bazuwar cutar.

A Najeriya ma, ministan lafiya na kasar Isaac Adewole, ya shawarci jami'an kiwon lafiya da jama'ar kasar baki daya, dasu gaggauta sanar da duk wata alama da suka samu dake nuna alamun cutar ga jami'an kula da lafiya.

A Rwanda ma, tuni aka kaddamar da shirin yin gwaje-gwaje a kan iyakokin kasar da Jamhuriya Demokuradiyyar Congon, domin gano masu dauke da kwayoyin cutar.

Tanzania ta tura tawagar jami'an kiwon lafiya zuwa yankuna shida a wani mataki da tattara duk wasu muhimman bayanai dake da nasaba da barkewar cutar ta Ebola.

Hukumomin kiwon lafiya a kasar Zambia sun tsaurara matakan tsaro kan iyakokin kasar da DRC. Ministan lafiya na kasar Chitalu Chilufya ya ce, gwamnati ta dauki dukkan matakai da suka dace domin hana cutar shiga kasar ta Zambia.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China