Gwamnatin Najeriya ta bukaci 'yan kasar, da su kai rahoton duk wasu alamu na zazzabi mai sanya zubar jini, tare da fadakar da juna game da wannan cuta, domin kaucewa bullar cutar Ebola, wadda tuni aka tabbatar ta kama wasu mutane a janhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC.
Cikin wata sanarwa da ministan lafiyar Najeriya Isaac Adewole ya fitar jiya a birnin Lagos, an ja hankulan cibiyoyin kiwon lafiyar kasar da su wayar da kan al'ummar kasar, tare da gabatar da rahoton bullar duk wata cuta dake iya zama babbar barazana ga mahukuntan kasar.
Mr. Adewole ya kara da cewa, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta tabbatar da bullar cutar Ebola a janhuriyar dimokaradiyyar Congo, wanda hakan ya sanya gwamnatin Najeriya kafa cibiyoyin tantance mutane a kan iyakokin ta, domin sanya ido tare da dakile shigar wannan cuta ta Ebola mai saurin kisa.(Saminu)