Kasar Tanzania ta tura tawagar kwararrun likitoci a shiyyoyi 6 na kasar domin ci gaban da daukar matakan na killacewa da kuma samar da muhimman bayanai don dakile yaduwar annobar cutar Ebola.
Wani kusa a gwamnatin kasar ne ya tabbatar da hakan, inda ya bayyana cewa, matakin da Tanzania ta dauka ya zo ne kwanaki 3 bayan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC a matsayin kasar da annobar cutar Ebola ta barke.
Mpoki Ulisubisya, babban sakatare a ma'aikatar lafiya da ci gaban al'umma ta kasar, ya bayyana cewa, an tura jami'an kiwon lafiyar ne zuwa yankunan Mwanza, Kagera, Kigoma, Katavi, Rukwa and Songwe.
Jami'in ya ce, sun dauki wannan mataki ne saboda suna cikin babbar barazana kasancewa mutanen dake dauke da kwayar cutar ta Ebola za su iya shigowa kasar ta wadannan yankuna, don haka ya zama tilas a dauki matakan da suka dace.
Ulisubisya ya ce, a dukkan hanyoyin wucewa da suka hada kasar Tanzaniya da DRC, dole ne a gudanar da bincike kan jama'a ko suna dauke da kwayoyin cutar.(Ahmad Fagam)