in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira da a kara kokarin fitar da nakasassu daga talauci
2018-05-10 20:36:09 cri

Gamayyar kungiyoyin nakasassu ta kasar Sin (CDPF) ta sanar a yau Alhamis cewa, babu wani mai nakasa da za a bari a shirin kasar na kawar da talauci.

Jami'in watsa labarai na gamayyar ta CDPT Guo Liqun wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, ya ce kimanin nakasassu miliyan biyar ne suka yi adabo da talauci cikin shekaru biyar din da suka gabata.

A shekarar 2017 kadai, kimanin masu nakasa 925,000 aka fitar daga kangin talauci, baya ga masu fama da wannan lalura miliyan 9.42 da aka dauka aiki a karshen shekarar.

Jami'in kawar da talauci na gamayyar Xie Hongde, ya ce har yanzu akwai masu fama da nakasa miliyan 2.81 dake cikin kangin talauci. Ya ce, abubuwan da gamayyar za ta tallafa sun hada da inganta ayyukan samar da hidima, da taimakawa yaran nakasassu ci gaba da karatu, da samar da jinya ga nakassun dake fama da talauci.

Kasar Sin dai tana fatan gina al'umma mai matsakaicin wadata nan da shekarar 2020, kuma cimma nasarar hakan na bukatar kawar da talauci. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China