in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban Jami'in kasar Sin ya bukaci a kyautata ingancin aikin rage talauci
2018-02-24 12:34:59 cri

Wani babban jami'in gwamnatin kasar Sin, ya ce kamata ya yi a kyautata ingancin aikin yaki da ake da talauci a kasar.

Wang Yang, wanda mamba ne a kwamitin zartarwa na hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya yi wannan jawabi ne yayin da yake jagorantar taron kwamitin majalisar zartarwar kasar kan rage talauci

Jami'in ya ce duk da nasarorin da aka cimma a yaki da ake da talaucin, har yanzu da sauran rina a kaba.

Ya ce dole ne a inganta aikin rage radadin talauci ta hanyar magance matsalolin da suke haifar da shi, sannan a kara kaimi wajen daukar matakan rage talaucin ta hanyar daukar managartan dabaru.

Kasar Sin na da niyyar kammala samar da al'umma mai matsakaicin ci gaba a dukkan fannoni daga nan zuwa shekarar 2020, wanda ke bukatar kawar da talauci.

Domin cimma wannan, kasar Sin na bukatar fitar da mutane sama da miliyan 10 daga kangin talauci a ko wace shekarar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China