Bisa ga wannan alkaluma, ana tsame mutane miliyan 13 ke nan a duk shekara daga kangin fatara. Matakin yawan talauci a kasar ya ragu matuka daga kashi 10.2 a shekarar 2012 inda ya koma kashi 3.1 bisa 100 a shekarar 2017.
Kasar Sin ta himmatu wajen kawar da talauci a kasar nan da shekarar 2020 a kokarinta na samar da wata al'umma mai matsakaiciyar wadata.
A karshen shekarar da ta gabata, akwai Sinawa kimanin miliya 30 dake rayuwa a kasa da mizanin karfin tattalin arziki na kasar.
Masana harkokin tsare-tsare na kasar Sin sun ayyana yaki da talauci da cewa yana daya daga cikin manyan batutuwa uku da kasar ke kokarin tunkararsu nan da shekaru 3 masu zuwa, sauran su ne rigakafin bala'u da kuma yaki da hayaki mai gurbata yanayi. Shekarar 2018 muhimmiyar shekara ce.
Sama da mutane miliyan 10 ne za'a tsame daga kangin fatara a shekarar 2018. Kimanin yankuna 100 na kasar ne ake sa ran tsamewa daga kangin talauci, in ji hukumar yaki da talaucin. (Ahmad Fagam)