Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Manoah Esipisu, ya fadawa 'yan jaridu cewa, aikin samar da gidajen masu saukin kudi ya hada da samar da gidaje kimanin 5,000 a yankin Shauri Moyo, da gidaje 20,000 a Makongeni, da 3,000 a Starehe da kuma gidaje 2,000 a hanyar rukunin gidaje na Park Road.
Esipisu ya ce, sashen dake kula da aikin farfado da ci gaban birnin Nairobi ya sha alwashin gudanar da aikin cikin watanni 6.
An yi kiyasin cewa ana fama da matsalar karancin gidaden sama da 250,000 a cikin wannan shekarar, koda yake kamfanonin dake aikin samar da gidaje a kasar za su iya samar da gidajen da adadinsu ya kai dubu 50 a duk shekara.
Esipisu ya ce an riga an kammala shirye shirye inda kamfanin samar da gidaje na Kenya Mortgage Refinance Company ya tsara takardun yarjejeniyar samar da gidaje a farashi mai sauki. (Ahmad Fagam)