in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a baiwa 'yan Afrika da suka yi fice a fannin fasahar makamashi lambar yabo
2018-04-18 09:54:22 cri
Kanana da matsakaitan kamfanoni masu yawa daga nahiyar Afrika da suka yi fice a fannonin samar da makamashi, da gine-gine, da kiwon lafiya da sufuri, da bangaren kudi ne za'a baiwa lambar yabo ta kasa da kasa kamar yadda jami'an da suka shirya bikin suka tabbatar da hakan a ranar 17 ga watan.

Wadanda aka zaba din daga Afrika za su yi gogayya da takwarorinsu na sauran sassan duniya a bikin bada lambar yabo na "2018 International Ashden Awards", wanda aka shirya da nufin karrama wadanda suka yi fice a fasahar samar da sinadarai daga tsirrai.

A wannan shekara an zabo wadanda za su karbi lambar yabon na Ashden ne sakamakon irin gudunmawar da suka bayar wajen samar da sinadarai masu rage dumamar yanayi, da kawo sauye sauye a yanayin zaman rayuwar al'umma game da kalubalolin albarkatu dake fuskantar al'umma a kasashen dake yankin kudu da hamadar Saharar Afrika.

A kasashen yammacin Afrika, wata kungiya mai rajin taimakawa yadda za'a yi kyakkyawan amfani da fasahar Nubian Vault wajen yin gine gine inda za a maye gurbin yin amfani da katato, tana daga cikin kungiyoyin da za su karbi lambar yabon.

Sauran wadanda za su karbi lambar yabon ta kasa da kasa daga Afrika sun hada da kamfanin KopaGas wanda yake bada gudunmowa wajen amfani da makamashin girki mai tsabta, da Lumos Global wani babban kamfani daga Najeriya wanda ke samar da lantarki ta hanyar amfani da hasken rana.

Kwamitin shirya bada lambar yabon na Ashden ya ce, jerin sunayen kamfanonin da za'a baiwa lambar yabon suna fuskantar tantancewa mai tsanani daga kwamitin kwararru da aka kafa gabanin bayyana wadanda suka yi nasara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China