A safiyar yau Laraba, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana a yayin taron ganawa tsakanin shugabannin Sin, da Japan da Koriya ta Kudu cewa, ya kamata sassan su ci gaba da gudanar da shawarwari, domin warware sabanin dake tsakaninsu, kuma kasar Sin tana goyon bayan kasar Koriya ta Arewa da kasar Koriya ta Kudu, a fannin kyautata dangantakar dake tsakaninsu, tana taya su murnar cimma nasarar ganawar shugabanninsu a karo na uku, kuma tana fatan za a gudanar da ganawar shugaban kasar Amurka da na kasar Koriya ta Arewa cikin nasara.
Bugu da kari, Li Keqiang ya ce, kasar Sin tana goyon bayan bangarorin da abun ya shafa, da su karfafa shawarwari tsakaninsu domin warware sabani tun daga tushe, da kuma samun ci gaba a yunkurin warware matsalar zirin Koriya ta hanyar siyasa, da kafa tsarin shimfida zaman lafiya a zirin Koriya, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiyar dindindin a yankin baki daya. (Maryam)