Sanarwar da Fadar White House ta fitar ta ruwaito cewa, shugabannin biyu wato Trump da Moon, za su tattauna ne kan ganawar dake tafe tsakanin Shugaban Amurkar da na Koriyar ta arewa.
Ziyarar ta Shugaba Moon, ta biyo bayan ganawarsa da shugaba Kim a ranar 27 ga watan Afrilun da ya gabata, inda shugabannin biyu suka tabbatar da burinsu na kawar da makaman nukiliya baki daya daga zirin Koriya.
Ana sa ran Donald Trump zai gana da Kim Jung Un a cikin wannan watan ko kuma farkon watan Yuni. Trump ya shaidawa manema labarai a jiya cewa, tuni aka sanya ranar da Amurka da Koriya ta arewa za su tattauna a karon farko, kuma nan bada dadewa ba za a sanar. (Fa'iza Mustapha)