in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An kammala tagwaita halittar jan biri nau'in macaques daga fasahar tinkiyar Dolly
2018-01-25 09:35:48 cri

Masu binciken kimiyya na kasar Sin sun ce, sun cimma nasarar tagwaita halittar wasu jan biri guda biyu nau'in macaques, bisa kimiyyar da aka yi amfani da ita wajen tagwaita tinkiyar Dolly.

Tagwaita halittar macaques dai ita ce irin ta ta farko da aka cimma nasarar aiwatarwa a duniya tun bayan tunkiyar Dolly, kuma hakan ya bude wani sabon shafi a fagen tagwaita halittun dabbobi daga zababbun kwayoyin halitta.

Biran masu suna Zhong Zhong da Hua Hua, an samar da su ne a cibiyar binciken dabbobi dake karkashin cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin ko CAS a takaice a karshen shekarar 2017. Ana kuma fatan kammala aikin biri na 3 nan gaba cikin watan nan na Janairu, za kuma a kara samar da wasu cikin shekarar nan ta 2018.

Tun bayan kammala tagwaita tinkiyar Dolly daga kwayoyin halittar babbar tinkiya a shekarar 1997, an gudanar da makamancin wannan aiki kan wasu dabbobin na daban, to sai dai kuma birin macaques shi ne mafi kusanci da halittar bil Adama da aka gudanar da wannan aiki a kan sa, wanda kuma aikin sa ke cike da kalubale.

An wallafa sakamakon binciken a mujallar kimiyya ta Cell.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China