in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya tattauna da shugaba Trump na Amurka ta wayar tarho
2018-05-09 09:26:37 cri
Bisa gayyatar da aka yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta wayar tarho a jiya Talata, da takwaransa na Amurka Donald Trump.

Xi Jinping ya nuna cewa, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka na cikin wani muhimmin lokaci, inda ya ce yana mayar da hankali sosai kan yadda ake bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kana yana girmama kyakkyawar dangantakar dake tsakaninsa da Shugaba Trump. Har ila yau, ya ce yana fatan bangarorin biyu, za su bi matsaya daya da suka cimma a lokacin ganawarsu a Beijing, tare da kara ci gaba da yin mu'amala tsakanin mutanen dake matakai daban-daban na kasashensu, ta yadda za a iya kara sa ido kan hadin gwiwarsu da daidaita bambance-bambancen bisa ka'idojin mutuntawa da moriyar juna, domin ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba cikin kwanciyar hankali kamar yadda ake fata. Mr. Xi ya kara da cewa, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ta kan kasance kamar tubali da jigon dake bunkasa dangantaka tsakanin Sin da Amurka. A makon jiya ne a birnin Beijing, bangarorin Sin da Amurka suka tattauna ba tare da boye komai ba, kan batun tattalin arziki da cinikayya. Shugaba Xi ya ce tawagogin bangarorin biyu, za su iya kara yin mu'amala a kokarin samun dabarun kawar da matsalolin da ke kasancewa tsakanin bangarorin biyu kamar yadda ya kamata, ta yadda za a iya samun sakamakon moriyar juna.

A nasa bangaren, Mr. Donald Trump ya bayyana cewa, bangaren Amurka ma na mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakaninsa da Sin. kuma yana sa ran kara yin mu'amala da shugaba Xi Jinping. Ya ce bangaren Amurka na fatan yin kokari tare da bangaren Sin, domin kara yin hadin gwiwar a zo a gani a fannoni daban daban, ta yadda za a iya daidaita batun tattalin arziki da cinikayya dake kasancewa a tsakanin kasashen biyu. Da kuma kokarin ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen gaba, domin kawo alheri ga al'ummominsu.

Sannan shugabannin kasashen biyu, sun yi musayar ra'ayi kan halin da ake ciki a yankin Koriya, inda shugaba Xi Jinping, ya nanata matsayin da kasar Sin ke dauka kan batun yankin Koriya, inda ya jaddada cewa, bangaren Sin na goyon bayan ganawar da za a yi tsakanin shugabannin kasashen Amurka da Koriya ta arewa, yana mai fatan bangarorin biyu za su yi kokari tare, ta yadda za su iya kafa wani tsarin amincewa da juna, da daukar matakai a kai a kai domin kokarin daidaita batutuwan da kowanensu ke mai da hankali a kai, ta hanyar ganawa da kuma shawarwari. Bugu da kari, Mr. Xi yana fatan bangaren Amurka, zai mai da hankali kan batun tsaro da bangaren Koriya ta arewa ke mai da hankali a kai, ta yadda kasashen 2 za su iya daidaita batun yankin Koriya a siyasance. Shugaba Xi Jinping ya tabbatar da cewa bangaren Sin zai ci gaba da taka rawar da ta dace a kokarin cimma burin kawar da nukiliya daga yankin Koriya da kuma tabbatar da kwanciyar hankali har abada a yankin.

Haka kuma, Mr. Trump ya bayyana cewa, bangaren Amurka na mai da hankali sosai kan matsayin da bangaren Sin ke dauka kan batun yankin Koriya, har ma ya yaba da muhimmiyar rawar da bangaren Sin ke takawa. Mr. Trump ya ce, yana son kara yin mu'amala da tattaunawa da bangaren Sin domin daidaita batun yankin Koriya ta hanyar shawarwari da tattaunawa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China