in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya jinjinawa ma'aikatan da suka zama abin koyi
2018-04-30 21:05:21 cri
A gabannin zuwan ranar 1 ga watan Mayu, wato ranar bikin kwadago ta duniya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar daliban dake karatu a kwalejin dangantakar kwadago ta kasar Sin, wadanda ke kasancewa ma'aikatan da suka zama abin koyi na kasar, inda ya taya duk ma'aikatan kasar murnar bikin wannan rana.

A cikin wasikar kuma, Xi ya yi fatan wadannan ma'aikatan da suka zama abin koyi, za su kara kokarin koyon ilimi, tare kuma da ci gaba da samun maki mai kyau a matakan ayyukansu. Ya jaddada cewa, ya kamata duk al'umma su girmama ma'aikatan da suka zama abin koyi, da kuma yada ra'ayinsu game da ayyuka.

Domin baiwa ma'aikatan da suka zama abin koyi damar samun ilmi a jami'a, a shekarar 1992, kwalejin dangantakar kwadago ta kasar Sin ta kafa kwas na musamman, don karbar ma'aikatan da suka zama abin koyi, da nagartattun ma'aikata bisa matsayin kasa. Kwanan baya, daliban da suka yi wannan kwas sun rubuta wasika ga shugaba Xi, inda suka bayyana ra'ayoyinsu game da tunanin shugaba Xi, bisa tsarin mulki na gurguzu mai hayalayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, kana sun bayyana niyyarsu ta taka rawar gani wajen raya kasar a sabon zamani. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China