Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban rundunar askarawar kasar, ya bayyana hakan ne Jumma'ar nan yayin babban taron cika shekaru 200 da haihuwar Karl Marx.
Shugaba Xi ya ce Karl Marx jagoran juyin-juya halin talakawa da ma ma'aikata a fadin duniya, kana mutumin da ya assasa ra'ayin da ma Jam'iyyar Markisanci, kana wanda ya gano turba kwaminisanci a duniya, kuma mai zurfin tunani a zamanin da muke ciki.
Ya ce, babban jarin da Marx ya barwa al'umma, shi ne ra'ayin da al'umma ke amfani da shi a yau, wato Markisanci. Kamar wani haske rana, ra'ayin ya haske wata hanya da al'umma ta yi amfani da wajen gano tarihin doka, da yadda al'umma za ta zabi hanyar 'yantar da kanta. (Ibrahim Yaya)