in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya na duba yiwuwar daidaita matsalar biyan haraji fiye da daya
2018-05-05 15:45:09 cri
Hukumar tattara kudin shiga ta Nijeriya FIRS, ta ce nan bada jimawa ba, za ta warware matsalar biyan haraji fiye da daya a jihohin kasar.

Shugaban hukumar, Babatunde Fowler ne ya sanar da shirin, yayin wani taron karawa juna sani kan mata da bangarori masu zaman kansu, wanda ya gudana jiya a Abuja babban birnin kasar.

Babatunde Fowler, ya shaidawa mahalarta taron cewa, hukumarsa ta fara kokarin daidaita matsalolin haraji a wani yunkuri na rage matsalar biyan haraji fiye da sau daya.

Ya ce wannan zai ba 'yan Nijeriya damar sanin ainihin haraji da ya kamata su biya, yana mai zargin yawancin jihohi da amfani da sunan hukumar FIRS wajen karbar haraji daga al'umma.

Babatunde Fowler, ya ce jihohi ne ke kakaba galibin harajin da 'yan Nijeriya ke korafi kansu, musammam mata 'yan kasuwa, amma ba hukumarsa ba.

Ya kara da cewa, ita ma hukumar dake kayyade haraji ta kasar na aiki tukuru domin daidaita matsalolin da suka shafi harajin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China