in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NNPC ya sanar da manufofin kawo karshen yadda ake asarar iskar gas a kasar
2018-05-04 12:49:17 cri

Jaridar Daily Trust ta kasar Nijeriya ta labarta jiya Alhamis cewa, babban darektan kamfanin NNPC Maikanti Baru ya bayyana a yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar a kwanan baya cewa, a cikin shekaru 10 da suka wuce, yawan iskar gas da ake asara a kasar Nijeriya ya ragu zuwa kashi 10 cikin dari daga kashi 25 cikin dari. Kamfanin ya kuma sanar da matakai guda 3, a kokarin dakatar yadda kasar ke asarar iskar gas.

Da farko, kamfanin ya bukaci hukumomin da suka gudanar da ayyukan hakar iskar gas da su mika shirye-shiryen hakar iskar gas na FDP da kuma shirye-shiryen yin amfani da iskar gas duka ga ma'aikatar dake samarwa da kayyade farashin man kasar DPR, ta yadda za a tabbatar da cewa, ba za a yi asarar iskar gas din yayin da ake gudanar da wadannan ayyuka yanzu da kuma nan gaba ba. Na biyu kuma, za a tanadi matakai na musamman dangane da manufar kasar kan iskar gas, da cin tarar kudi kamar yadda dokar kawo karshen asarar iskar gas ta NGFCP ta shekarar 2016. Na uku kuwa, za a kawo karshen asarar iskar gas bisa ka'idojin yaki da asarar iskar gas na shekarar 2018. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China