Kafar yada labarai ta kasar ta ruwaito Assefa Abyou na bayyana haka a jiya, inda ya ce tun bayan sanya dokar a ranar 16 ga watan Fabreru, harkokin kasuwanci da na sufuri da a baya ke fuskantar tarnaki saboda hare-hare da zanga-zanga, sun daidaita.
Sai dai, Kwamishinan ya tabbatar da cewa al'umma na fargaba sake dawowar rikici duk da cewa harkokin yau da kullum a yankunan karkara da birane sun dawo kamar yadda suke. (Fa'iza Mustapha)