A kwanan baya ne wani kamfanin kasar Sin Poly-GCL, ya gano iskar gas wanda yawansa ya kai cubic trillion feet (TFC) biliyan 7 zuwa 8 a jahar yankin Somali dake kasar ta Habasha.
Ministan ma'adanai da albarkatun man fetur da iskar gas na kasar Motuma Mekassa, an rawaito kalamansa a cikin wata jaridar kasar data wallafa yana mai cewa, suna sa ran samun dala biliyan guda na kudin shiga a shekara daga iskar gas din da zasu fitar zuwa ketare a shekarar farko da fara aikin, kuma ana hasashen cewa adadin zai iya karuwa sannu a hankali a cikin shekaru masu zuwa a nan gaba, sakamakon yawan adadin albarkatun iskar gas din dake jibge a yankin.
Mekassa ya ce, gano albarkatun iskar gas din babban cigaba ne wanda ake sa ran zai bayar da gagarumar gudunmowa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar cikin sauri a shekaru masu zuwa. (Ahmad Fagam)