in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta tallafawa shirin WFP a Habasha da makudan kudade
2018-03-14 09:47:20 cri
Gwamnatin kasar Sin ta baiwa shirin hukumar abinci ta MDD (WFP) dake aiki a kasar Habasha tallafin kudade har dalar Amurka miliyan 6, don tallafawa yankunan kasar dake fama da fari, da ma masu gudun hijira da kasar ke taimakawa.

Tallafin na wannan karo dai shi ne irin sa na 4 da Sin ta samar ga kasar dake gabashin Afirka, wadda baya ga 'yan kasar ta, take kuma taimakawa masu samun mafaka daga kasashe makwaftan ta.

Da yake tsokaci game da hakan, jakadan Sin a Habasha Tan Jian, ya ce ya gamsu da kwazon da Habasha ke yi a wannan fanni, kuma bai kamata kasashen duniya ciki hadda kasar Sin, su yi kasa a gwiwa wajen ba da nasu tallafi ba.

An kiyasta cewa, akwai kimanin 'yan kasar ta Habasha miliyan 7.9 dake cikin matsananciyar bukatar taimakon abinci, yayin da kasar ke ci gaba da baiwa masu gudun hijira sama da 900,000 mafaka.'Yan gudun hijirar dai sun fito ne daga kasashen Eritrea, da Sudan ta kudu da Somalia, da kuma Sudan.

Shirin abinci na MDD ya ayyana cewa, da wannan tallafi na kasar Sin, zai samar da taimakon watanni 2 ga mutane da yawan su ya kai 350,000, ciki hadda wadanda ke zaune a yankunan da fari ya shafa da shinkafa har sama da tan 4,000, da man girki tan 800.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China