in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudaden shigar Habasha daga bangaren masana'antu ya karu da dala miliyan 42 cikin watanni 6
2018-04-01 12:33:13 cri
Wani jami'in kasar Habasha ya tabbatar da cewa, kasar ta samu karin kudaden shigarta na kayayyakin da take fitarwa daga rukunin masana'antu zuwa ketare wanda ya tasamma dalar Amurka miliyan 42 cikin watanni 6 na shekakarar 2017/18 wanda ta fara daga ranar 9 ga watan Yuli ta shekarar 2017.

Da yake magana da 'yan jaridu, Fitsum Arega, kwamishinan hukumar zuba jarin kasar Habasha ya bayyana cewa, kamfanonin dake gudanar da ayyukansu a rukunin masana'antun kasar ya samar da guraben ayyukan yi ga 'yan kasar Habasha su kimanin dubu 50.

Ya kara da cewa, an riga an kaddamar da rukunin masana'antu na Hawassa, yayin da rukunin masana'antu na Kombolcha da Mekelle su ma sun fara kwarya-kwaryar aiki, yayin kuma aka kammala aikin gina rukunin masana'antun Adama da Dire Dawa.

Arega ya yabawa kamfanonin kasar Sin da suka zuba jari a Habasha, wanda ya bayyana cewa babban ci gaba ne ga kasar Habashan, da kuma burin da kasar ke da shi na samar da guraben aikin yi ga wadanda suke bukatar ayyukan yi daga cikin 'yan kasar su kimanin miliyan 100. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China