in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan a warware rikicin Libya a siyasance
2018-04-16 13:57:53 cri
Mukadashin jakadan kasar Sin dake Libya Wang Qimin ya zanta da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Lahadi, inda ya bayyana cewa, Sin na goyon bayan a warware matsalar Libya a siyasance, kuma Sin na fatan za a kyautata halin da ake ciki a Libya tun da wuri.

A wannan rana kuma, Wang Qimin ya gana da sabon shugaban kwamitin koli na kasar Libya Khaled Al-Meshri, mambar jam'iyyar adalci da raya kasa ya zama shugaban kwamitin a ranar 8 ga wannan wata, an ce wannan kwamiti dai ya samu amincewa daga kasashen duniya wanda ya ba da shawara ga dunkulewar al'ummar Libya.(Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China