A cewar kakakin hukumar kwallon kafa ta Libya, Fatih Halbus, ayarin jami'an FIFA sun isa kasar inda za su yi ziyarar yini 3, don hada cikakken rahoton kan yanayin tsaro da na kayaki a filayen wasan kasar, da nufin dage haramcin buga wasan kungiyoyin kasashen waje a filayen wasan da aka yi a shekarar 2013.
Kakakin ya tabbatar da cewa, ziyarar wani bangare ne na goyon bayan da hukumar FIFA ke ba hukumar kwallon kafa ta kasar.
Tun a shekarar 2013, FIFA ta haramta gudanar da wasanni da suka shafi kasashen waje a filayen wasan Libya saboda tabarbarewar tsaro a kasar. (Fa'iza Mustapha)